Amfanin bawon rumman:
1- Bawon Ruman yana maganin gyambon ciki (Stomach Ulcer).
2- Yana maganin ciwon duodenal ulcer.
3- Ana amfani da shi wajen magance kumburin yar wuya (tonsillitis).
4- Ana amfani dashi wajen maganin zazzabi.
5- Bawon Ruman yana maganin basur.
6- Yana daya daga cikin mafi kyawun maganin zawo.
7- Ana amfani da shi wajen magance yawan yin zufa.
8- Ana amfani dashi wajen samun hasken hakora (garin bawon rumman + garin Gawayi + gishiri + toothpaste + zuma).
9- Yana taimakawa wajen magance warin baki.
10- Yana maganin tsutsotsi.
11- Yana taimakawa wajen magance rauni.
12- Ana amfani da shi wajen magance kurajen fuska da cututtukan fata.
13- Ana amfani da shi wajen gyaran gashi da gyaran launinsa.
14- Ana amfani da shi wajen samun hasken fata.
15- Ana amfani da shi ga masu mouth ulcer.
Yadda ake amfani da shi:
Babban cokali 2 na garin bawon rumman.
A hada shi a cikin zuma 200g sai a sha karamin cokali guda sau daya a kullum.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
ALLAH YA KARBI IBADUN MU.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
Comments
Post a Comment