AMFANIN NONON RAƘUMI (Kashi na biyu) (8)CIWON SUGA. Mai fama da larurar ciwon suga sai a samo: - a) Nonon Raƙumi kofi daya. b) Tirmis Baladi, cikin ƙaramin cokali c) Garin Hulba, karamin cokali d) Hubuwbul liƙah ƙaramin cokali e)Markadadden bitter lemon ƙaramin cokali. Sai a kaɗa su a cikin nonon, sai a sha kofi daya da safe kofi daya da yamma tun kafin a ci abinci da awa daya, ma'ana idan an sha maganin sai an samu awa đaya a tsakani sannan za a ci wani abu. (9) CIWON CANCER Wanda yake da wani ciwo da ya shafi cancer to sai ya yi kokarin jarraba wannan maganin: Zai rika shan kofi daya na nonon rakumi da safe da yamma amma tun kafin ya ci wani abu da awa daya. Ma'ana, ba zai ci wani abu ba zai sha maganin. Idan kuma ya sha maganin to sai ya Samu awa daya a tsakani, sannan zai ci wani abu. Za a yi haka a jere ba fashi tsawon kwana arba'in da biyar. Sannan duk sanda ya sha wannan nonon to zai sha shayin lipton ba madara cikin babban kofi tare da rabin...