AMFANIN NONON RAƘUMI (Kashi na biyu) (8)CIWON SUGA. Mai fama da larurar ciwon suga sai a samo: - a) Nonon Raƙumi kofi daya. b) Tirmis Baladi, cikin ƙaramin cokali c) Garin Hulba, karamin cokali d) Hubuwbul liƙah ƙaramin cokali e)Markadadden bitter lemon ƙaramin cokali. Sai a kaɗa su a cikin nonon, sai a sha kofi daya da safe kofi daya da yamma tun kafin a ci abinci da awa daya, ma'ana idan an sha maganin sai an samu awa đaya a tsakani sannan za a ci wani abu. (9) CIWON CANCER Wanda yake da wani ciwo da ya shafi cancer to sai ya yi kokarin jarraba wannan maganin: Zai rika shan kofi daya na nonon rakumi da safe da yamma amma tun kafin ya ci wani abu da awa daya. Ma'ana, ba zai ci wani abu ba zai sha maganin. Idan kuma ya sha maganin to sai ya Samu awa daya a tsakani, sannan zai ci wani abu. Za a yi haka a jere ba fashi tsawon kwana arba'in da biyar. Sannan duk sanda ya sha wannan nonon to zai sha shayin lipton ba madara cikin babban kofi tare da rabin...
Amfanin bawon rumman: 1- Bawon Ruman yana maganin gyambon ciki (Stomach Ulcer). 2- Yana maganin ciwon duodenal ulcer. 3- Ana amfani da shi wajen magance kumburin yar wuya (tonsillitis). 4- Ana amfani dashi wajen maganin zazzabi. 5- Bawon Ruman yana maganin basur. 6- Yana daya daga cikin mafi kyawun maganin zawo. 7- Ana amfani da shi wajen magance yawan yin zufa. 8- Ana amfani dashi wajen samun hasken hakora (garin bawon rumman + garin Gawayi + gishiri + toothpaste + zuma). 9- Yana taimakawa wajen magance warin baki. 10- Yana maganin tsutsotsi. 11- Yana taimakawa wajen magance rauni. 12- Ana amfani da shi wajen magance kurajen fuska da cututtukan fata. 13- Ana amfani da shi wajen gyaran gashi da gyaran launinsa. 14- Ana amfani da shi wajen samun hasken fata. 15- Ana amfani da shi ga masu mouth ulcer. Yadda ake amfani da shi: Babban cokali 2 na garin bawon rumman. A hada shi a cikin zuma 200g sai a sha karamin cokali guda sau daya a kullum. ALLAH YA BAWA DUK WASU M...